A jiya an fafata wasannin rana ta 4 a gasar share fage ta gwamna Aminu Masari dake gudana a filin wasa na Mjhammadu Diko dake jahar ta Katsina.
Jiyan wasu kungiyoyin kwallon kafar sun huce haushin cin da akayimusu a rana ta 2 data 3.
Ga sakamakon wasannin kamar haka:
Zamfara 0 – 0 Rarara Academy
Sokoto United 2 0 Junior Katsina United
Garkuwa 1 4 Plateau United.
Katsina United 0 – 0 Wikki Tourists
A jiya akajiyo mai horas da ƙungiyar ƙwallon kafa ta Plateau United wato Audu Maikaba yana cewa shifa dole ‘yan wasansa su gyara ganin yadda Niger Tornadoes ta lallasasu daci 2 da nema awasan rana ta 3. Sai gashi ‘yan wasan sunji kiran da yayi agaresu sun jefa ƙwallaye 4 a jiya.