A ci gaba da fafata wasannin gasar ƙwallon hannu wato gasar ajin Firimiya ta ƙasar nan wasannin kakar wasa ta 2020, a yamnacin wannan rana an fafata wasanni masu zafi.
Inda aka fafata wasannin a babban birnin tarayya Abuja inda acan ake gudanar da gasar ta wannan shekarar.
Kakar wasan dai ana fafata wasannin ɓangaren maza dana ɓangaren mata kuma wasannin suna ƙayatarwa yadda ya kamata. A kakar wasan data gabata dai ƙungiyar ƙwallon hannu ta Kano Pillars ce ta zamo zakara.
Ga jerin sakamakon wasannin da aka fafata a wannan yammaci na Litinin.
Wasannin ɓangaren mata:
Adorable Angels 33 – 36 Defender Babes.
Desert Queens 16 – 23 Seasider Babes.
A wasannin ɓangaren maza kuwa:
Borno Spiders 26 – 26 Lagos Seasiders.
Kada Stars 19 – 23Plateau Vipers.
D:Defenders 29 – 22 Rima Strikers.
A gobe Talata za a shiga rana ta 4 a wasannin gasar ƙwallon hannun ta ajin Firimiya mai taken Prudent Energy bayan da aka kammala wasannin rana ta uku a yau.