Kocin Tottenham Jose Mourinho ya bayyana cewa, ba zai yiwu ya farata wa daukacin ‘yan wasansa rai ba bayan sun yi nasarar doke Royal Antwerp, abin da ya ba su damar samun gurbi a gasar Europa, matakin kungiyoyi 32.
Mourinho ya ci gaba da amfani da ‘yan wasansa 11 da ke bugawa masa gasar firimiya akai akai a wannan kaka, ganin yadda suke yi masa abin da yake muradi.
Kodayake a wasansu na jiya Alhamis a gasar Europa, kocin ya dan hutar da zaratan ‘yan wasansa kamar Harry Kane da Son Heung-min da ke zura masa kwallaye a raga, inda ya bai wa irinsu Gareth Bale da Carlos Vinicius da Harry Winks damar taka leda.
Kocin ya ce, ‘yan wasan da ake ajiye su a banci basa jin dadin haka, amma kuma ya kamata su yi farin cikin nasarorin da kungiyar ke samu koda kuwa ba su buga mata wasa ba a cewarsa.