Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban jam’iyyar PDP na yankin Kauyen Kampala, da ke karamar hukumar Bosso, Ahmodu Mohammed wanda yake kauyen Madaka da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
An kashe Jigon na PDP a gidansa yayin da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da ‘ya’yansa mata uku a yayin da aka kashe Hakimin Kauyen mako guda bayan ‘yan ta’addan sun sace shi.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun dade suna bin Mohammed kafin a kashe shi a ranar Asabar. An gano cewa ‘yan bindigar sun kai 15 yayin da suke dauke da muggan makamai a lokacin da suka yi ta yin fada da mamacin har na tsawon awanni biyu.
Kuma an gano cewa an harbi marigayin da yawa kafin a kashe shi, kuma wannan harin shi ne karo na uku da ‘yan ta’addan ke kai wa Mohammed hari.
Tsohon shugaban jam’iyyar na jihar Neja, Alhaji Tanko Beji ya tabbatar da mutuwar Jigon na PDP da sace ‘ya’yansa mata. Sai dai ya ce har yanzu ba su ji daga bakin maharan ba game da ‘yan matan.
An kashe Hakimin Madaka a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, Zakari Ya’u Idris mako guda bayan sace shi. An fara satar Idris ne makonni kadan da suka gabata sannan aka sake shi kafin ‘yan bindigar su sace shi a ranar Lahadi, 20 ga Disamba 2020, kuma suka kashe shi mako guda bayan haka.
Shugaban Ma’aikatan Karamar Hukumar Rafi, Mohammed Mohammed ya tabbatar da kisan Zakari Idris inda ya kara da cewa an nemi N800, 000 daga dangin amma an kashe shi kafin a biya kudin fansa. Mohammed ya bayyana cewa karamar hukumar ta samu labarin mutuwar hakimin daga wasu mutanen da aka sace kuma aka sake su bayan sun biya kudin fansarsu. “Ya bayyana cewa Zakari ya mutu ne a lokacin da ‘yan fashin ke azabtar da shi, ko yaushe suna dukanshi” in ji Mohammed.
Ya ce an fadawa majalisar cewa ‘yan ta’addan sun binne gawar Idris a cikin daji. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Neja, ASP Abiodun Wasiu ba a iya jin ta bakin sa ba dangane da mutuwar mutanen biyu da ‘yan bindiga suka kashe ba.