Wani ma’aikacin kamfani, Kazeem Adebiyi, ya shaidawa wata kotun gargajiya da ke da zama a Ile-Tuntun a Ibadan cewa ta raba aurensa na shekaru hudu saboda masifaffiyar matarsa, Rukayat, wacce ke yawan yi masa barazanar kisa ta hanyar caka masa wuka.
Da ya ke yanke hukunci, shugaban kotun, Cheif Henry Agbaje, ya ce kotun ta warware wannan aure, domin wanzar da zaman lafiya tsakanin Adebiyi da Rukayat.
Agbaje ya kuma amince Rukayat ta ci gaba da kula da yayansu biyu tare da umurtar Adebiyi ya rinka biyanta N8,000 a kowanne wata domin kula da abincin yara, haka zalika zai ci gaba da daukar nauyin karatu da sauran bukatun yaran.
KARANTA WANNAN: Yadda Wani matsafi ya fille kan wani matashi tare da kwakule idanuwansa a Bauchi
Sai dai, Rukayat ta karya duk wannan zargi da mijinta ya ke yi mata, amma dai ta kasa kare kanta kan zarge zargen da mijin na ya yi mata.
A maimakon hakan, ta shaidawa kotun cewa yaransu kananu ne, za su iya shiga wani hali idan har aka raba auren.