A yunkurinsa na yin arziki cikin gaggawa, wani matashi mai shekaru 22, Musa Hamza, ya shiga komar ‘yan sanda biyo bayan zarginsa da fille kan wani matashi tare da daddatsa gabobin jikinsa a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya kwakule idon matashin, inda ya kona jikinsa da kansa, tare da binne wa a wani kabari da ya gina.
Wakil, mataimakin SP na rundunar ‘yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar daren ranar Litinin, ya bayyana cewa tuni rundunar ta tono sassan jikin matashin domin yin gwaji a asibiti.
KARANTA WANNAN: Zaben 2023: Tinubu na da ikon tsayawa takarar shugaban kasa, cewar Osoba
Ya ce: “A ranar 21 ga watan Disamba 2020, da misalin karfe 9:30am, jami’an ‘yan sanda na ofishin rundunar da ke Alkaleri, sun cafke Musa Hamza (22) na kauyen Unguwar Wake, karamar hukumar Alkaleri, wanda ja wani matashi Adamu Ibrahim (17) dan unguwarsu zuwa bayan gari, ya kashe shi tare da datse masa kai.
“Ta karfin tsiya ya kwakule masa idanu, tare da kona jikinsa da kansa, ya rufe shi a wani kabari da ya tona a cikin wani daji dake bayan garin.
“A yayin bincike, an tono dukkanin sassan jikin kuma an kai su babban asibitin Alkaleri domin yin bincike, inda kuma likitan ya tabbatar da cewa akwai wasu sassan jikin da aka cire.”
Ya kara da cewa, a yayin tuhumar wanda ake zargin, “an gano idanuwan biyu daga wanda ake zargin, wanda ya amince da aikata wannan laifi, inda ya shaida cewa, wani boka ne ya ce ya samo idanuwan domin yi masa asirin da zai zama attajiri cikin karamin lokaci.”een cut off with a sharp object.