Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai tare da kashe mutane 70 a Zaroumdareye, wani garin da ke iyaka tsakanin jamhuriyyar Niger da Mali.
Shugaban kasar ya magantu kan wannan harin ne a ranar Lahadi a Abuja, yana mai bayyana harin a matsayin wata alama ta nuna muhimmancin hadin kan shuwagabannin Africa wajen yaki da ta’addanci.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa ta hannun hadiminsa, Garba Shehu, ya ce, “Hakika na kadu matuka da irin adadin mutanen da ‘yan bindiga suka kashe, lallai wannan tsantsar rashin imani da tausayi ne ga rayuwar dan Adam.”
KARANTA WANNAN: Kullum sai matata ta yi mun barazanar kisa ta hanyar caka mun wuka – Miji ya koka gaban Kotu
A cewar shugaban kasar, “Muna fuskantar kalubale mai tarin yawa a yakin da muke yi da ta’addanci da ‘yan ta’adda, kuma har sai mun hada kawunanmu ne za mu iya kawo karshe wadannan kashe kashe.”
Ya yi nuni da cewa “Ta’addanci ya zama tamkar wata annoba mai iya yaduwa a kowanne lokaci ma damar bamu hada kawunanmu mun dakile hakan ba.”
Shugaba Buhari ya tariyo yadda aka samu rashin dai daito a kasar Libiya a shekarar 2011 inda ya jawo babbar matsala ga fannin tsaro da kai hare harin kasar, da sauran kasashen Afrika ciki har da Nigeria, Niger, Chadi da Kamaru da sauransu.
“Fasa dakin ajiye makamai da sace makaman da aka yi a Libiya bayan kifewar gwamnatin Gaddafi, ya jefa muggan makamai a hannun ‘yan ta’adda da kuma miyagun mutane, wadanda a yanzu suka zama ciwon idanu ga matsalar tsaron kasashen Afrika,” a cewar shugaban kasar.