Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni na kan gaba bayan soma ƙirga kuri’un zaɓen ƙasar, kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta fara fitarwa a safiyar Juma’a ya nuna.
Mista Museveni ya samu ƙuri’u 1,536,205 a halin yanzu (kashi 65.02 cikin 100) sai kuma abokin karawarsa Robert Kyagulanyi wanda aka fi sani da Bobi Wine ya samu ƙuri’u 647,146 (kashi 27.39) daga rumfunan zaɓe 8,310, sauran ƴan takarar kuma na da sauran kason.
Kasar dai na da jumullar rumfunan zaɓe 34,684.