Baya ga shirin gwamnatin tarayya na cin bashi a cikin gida Nijeriya da ma kasashen duniya comin cika kasafin kudin 2021, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta siyar da wadansu kadarorinta domin cika kudin kasafin.
Gwamnatin ta ce za ta siyar da wadansu kadarorin ne domin a samu karin kudin da za a zuba a cikin kasafin kudin shekarar.
Gwamnatin ta tabbatar da hakan ne ta hannun ministan kudi, Zainab Ahmed a yayin wani jawabi da ta yi wa masu ruwa da tsaki A Abuja kan kasafin kudin 2021.