Sarkin Musulmin Nijeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa al’ummar Fulani “ba ‘yan ta’adda ba ne”.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito sarkin na bayyana hakan ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ziyara a hukumar aikin hajji ta ƙasa NAHCON.
“Na faɗa a baya kan haka cewa mu ba ‘yan ta’adda ba ne ko miyagu,” a cewarsa. “Tabbas akwai ‘yan fashi daga cikinmu amma hakan ba zai sa a kira al’umma guda ko kuma Musulmai ‘yan fashi ba.”
Ya ƙara da cewa: “Ina alfaharin kasancewata Bafulatani kuma ko da a ce za a sake halittata bayan na mutu, wanda na san ba zai yiwu ba, zan roƙi Allah ya dawo da ni a matsayin Bafulatani.
“Ina alfaharin kasancewata Bafulatani amma ni ba ɗan ta’adda ba ne ko ɗan fashi.”
Kazalika ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa za a gudanar da aikin hajji na 2021 saboda allurar rigakafin cutar korona da aka samu kuma ya shawarci Musulmai da su bi dokokin kariya daga cutar, waɗanda gwamnati ke sakawa.