Kotu mai lamba ta 8 dake a Gyadi Gyadi karkashin mai Shari’a Ibrahim Khalil a yau Laraba ta sallami karar da aka gabatar mata na zargin Fatima Hamza mai shekaru 30 da kashe Yar’aikinta.
Bayan karbar sakamako na shawara daga ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, lauyan gwamnati Barister Muhammad Sani Ahamd ya nemi kotu da ta sallami wacce ake zargi Fatima bisa rashin gabatar da hujja a kan zargin.
A nasu bangaran lauyoyin wacce ake zargi ta bakin Barister Ibrahim Abdullahi Chedi bai kalubalanci wannan roko na lauyan gwamnati ba, inda ya nuna farin cikin sa da goyon baya a kan hakan.Daga karshe mai shari’a Ibrahim Khalil ya sallami karar bisa rashin wata hujja da zata tabbatar da zargin da ake akan Fatima.