Gwamnatin Tarayya ta bukaci jama’a da su tashi tsaye wajen ganin sun bada gudunmawar su don kare yawaitar aukuwar matsalar sace-sacen yan makaranta.
Karamin Ministan Ilmin Najeriya Chukwuemeka Nwajiuba wanda shine ya fadi haka a wata tattaunawa da Jaridar Punch, ya ce lallai fah gwamnati ita kadai ba ta isa iya kare ko ina ba.
A cewar shi, a yanzu haka tuni gwamnatin tarayya ta umarci dukkannin makarantu du su rika gaggauta kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ba ga cibiyoyin tsaro mafi kusa da su.
Yayin tattaunawar an jefa tambaya ga Ministan kan irin dabarun da gwamnati ke kokarin yi don kare makarantu daga hare-haren yan fashin daji.
Inda Ministan ya ce “Sanya idanu daga al’umma na taimakawa bmatuka. Ko wace kasa a fadin duniyuar nan na la’akari ne da yadda al’umma ke rayuwa. Gwamnatin tarayya ba za ta bi gida-gida tana bada tsaro ba. Dole kowa ya tashi tsaye. Mun Sanar da wannan sako ga dukkannin makarantu don idan suka ga wani yunkurin mabarnata su gaggauta isar da shi zuwa ga hukumonin tsaro.
Kazalika Nwajiuba ya ce kusan karan-kata-kaf din makarantu a fadin kasar nan an katange su, a cewar shi kama daga na gwamnati har ma da masu zaman kan su, ya ce duk makarantar da ba a katange ta ba to tsiraru ne kawai daga gwamnatocin jihohi.