Gwamnatin tarayya ta ce za ta gudanar da bincike tare da neman shawara gabannin sake cire tallafin Man Fetur, Kamar yadda Kamfanin dake Kula da Man Fetur ta Kasa (NNPC) ta bayyana.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Litinin ne Jaridar Punch ta ruwaito cewa NNPC zai kashe kudi kimanin Naira Biliyan Dari da biyu da digo chasa’in da tara (N102.96) a kan farashin man cikin wannan wata.
Har wa yau jaridar ta Punch ta bgano cewa na amfani da litar mai kimanin miliyan hamsin da bakwai da digo arbain da hudu (57.44 million litres) kowace rana, yayin da kudin ko wace lita daga depo yana a matsayin naira dari biyu da shida da kobo arba’in da biyu ne.
Toh sai dai Kamfanin NNPC na saida ta a kan naira dari da arba’in da takwas ko wace lita, inda gwamnatin tarayyar ta sha alwashin ci gaba da wannan tallafi har a kammala wannan wata na Maris.
Kimanin shekaru uku kenan dai da kamfanin NNPC ke kula da dawainiyar shigo da man fetur zuwa gida Najeriya.
Idan za a iya tunawa dai hukumar dake kula da Farashin Man Fetur din ta Kasa PPPRA ta wallafa farashin man na watan Maris din shekara ta 2021, inda farashin ya kai dari biyu da tara da kobo sittin da daya zuwa dari biyu da sha biyu da kobo sittin da daya.
Toh sai dai daga bisani hukumar ta soke wanchan jawabi tare da biyo baya da bayanin cewa ba wai hakan yana nufin za a fara saida shi a kasuwanni ba ne.