Wata Babbar Kotu dkae zaman ta Babban birnin tarayya Abuja ta dage zaman shari’ar da ake yi kan wata kara da aka shigar don tube Sufeta Janar na Yan Sandan Najeriya Muhammad Adamu.
Shari’ar wanda Justice Ahmad Muhammad ke jagoranta ta gamu da cikas ne sakamakon rashin bin lamarin sau da kafa daga hukumar kula da Yan Sanda ta kasa ta yi.
Ita dai wannan kara wani Lauya ne dake birnin tarayya Abuja mai suna Mr. Maxwell Okpara ya shigar gaban kotun biyo bayan umarnin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na tsawaita wa’adin Sufeta Janar din da wata uku bayan ritayar shi watan da ya gabata.
Ita dai Karar tana kira ne da Muhammad Adamu ya yi ritaya ganin cewa ya kammala adadin shekaru talatin da biyar yana murza aiki.
Lauyan dake kare yan sanda Dr. Alex Izinyon ya ce an dage karar ce don baiwa dukkanin bangarorin damar sake shiri, ya kara da cewa tuni shigar da korafin su ga shari’ar.
Toh sai dai Lauyan Masu shiga da Kara Mr. Ugochukwu Ezekiel ya ce su sam ba su gamsu da hukuncin kotun ba don haka za su sake duba wannan lamari.