Shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Isiaka Amao a ranar Laraba ya yi alkawarin murkushe ayyukan ‘yan ta’adda a arewa maso yammacin Nijeriya, inda ya ce kwanan nan za su murkushe ta’addancin.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyara a Barikin sojin Saman dake jihar Kaduna, inda ya gargadi ‘yan ta’adda da su shirya ma fuskantar hari mafi muni.
Ya ci gaba da cewa sojoji za su bi su har maboyar ‘yan bindigar da masu garkuwa da jama’a bisa bin umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda domin manoma su samu su koma gonakinsu ba tare da wata matsala ba.
Amao ya bada tabbacin cewa sojoji a shirye suke su murkushe ‘yan ta’adda a Nijeriya, harma da sauran bata gari dake hana kasarnan zaman lafiya.
Ya yi alkawarin amfani da makamai da jiragen sama na rundunar sojin saman wajen gudanar da ayyukansu.