An kammala buga wasannin gasar Zakarun Turai zagaye na 2 da ya kunshi kungiyoyi 16.
Yayin wasannin da aka karkare a ranar Laraba 17 ga watan Maris, Bayern Munich ta samu nasara kan Lazio da 2-1, sai Chelsea da ta doke Atletico Madrid da 2-0
Kungiyoyi 8 da suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen wasan kusa da kusa da na karshe na kwata final, sun hada da Chelsea, Bayern Munich, Manchester City, Liverpool, PSG, Real Madrid, Borussia Dortmund da kuma FC Porto.
Ranar Juma’a hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA za ta fitar da jadawalin kungiyoyin da za su kara da juna a zagayen na kwata final.
Taron fitar da jadawalin kuma zai gudana ne a birnin Nyon dake kasar Switzerland.