Kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya bayyana cewa cikin mako guda an yi wa mutum 15,959 allurar rigakafin korona a jihar ya zuwa ranar Laraba.
Dr Dahiru ya bayyana hakan ne a yayin hirarsa da manema labarai a Gombe jim kadan da wani taron kwana daya da aka shirya tsakanin shugabannin addini da ‘yan jarida akan muhimmancin allurer rigakafin korona din, wanda hukumar lura da lafiya a matakin farko na jihar Gombe ta shirya.
Kwamishinan ya ce mutum 15,959 aka yi wa allurar, wanda wannan adadin ya dauki kashi 44 na adadin wadanda za a yi wa allurer a matakin farko.
Kwamishinan ya ce suna da kwarin guiwar cewa za su cimma nasarrar da suka shimfida wajen yin rigakafin allurar korona din.
Kwamishinan ya ce an shirya zaman taron ne domin wayar da kan al’umma akan muhimman yin allurar.
“mun zabi shugabannin addini da ‘yan jarida ne saboda muhimmancinsu a cikin al’umma, wanda al’umma tana iya saurarensu”, ya lurantar.
Ya tabbatar da cewa; Allurar rigakafin kotona ta AstraZeneca yana da inganci da kashi 95, inda ya ce amfanin allurar ya fi illar allurar yawa.