Ministar Kudin Tarayya Zainab ahmad ta ce gwamnatin tarayyya ta kudiri aniyar bada muhimmannci a bangaren tsarin tazarar haihuwa da kuma bangaren lafiya kacokam dinsa don ganin an inganta rayuwar al’umma.
Ministar ta bayyana haka ne a yayin da ta karbi bakoncin wata tawaga daga kungiyar Mata Likitoci ta Kasa da hadin gwiwar Kungiyar dake rajin inganta lafiytar iyali a ofishin ta dake birinin tarayya abuja.
Ta tabbatar wa da tawagar cewa Ma’aikatar kdui za ta ci gaba da bada muhimmanci ga bangaren lafiya musamman kan matsaloli da suka shafi yarjejeniyar bangarori da kuma wasu shirin ayyuka da kasar nan ke yunkurin aiwatarwa.
Zainab Ahmad ta ce kalubale dake kawo cikas ga bangaren sanya kudade a Sassan da Hukumomin gwamnatin shine irin yadda ake almuzarranci da dukiyar kasa wanda ta ce hakan shike kashe gwiwa wajen ci gaba da zuba kudade a bangaroroin.
Tun farko da take jawabi Shugabar tawagar wacce kana ita ce shugabar Kungiyar mata Likitoci ta kasar Dakta Minnie Oseji ta tuantatr da Minsitar danagane da babban taron kungiyar ta kasa dake wkaana a halin inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dube su da idanun rahama.