Wani dan sanda a jihar Neja ya dambarawa wani dan bindiga da yake dauke da bindigar AK-47 harsashi, inda ya kashe shi nan take.
Lamarin ya auku ne a kauyen Tashan-Barau dake karamar hukumar Rafi a jihar ta Neja.
Adamu Usman, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar hakan a yayin zantawa da manema labarai a garin Minna a ranar Laraba.
Usman ya ce lamarin ya auku ne a ranar 30 ga watan Maris da misalin karfe 3 da minti 25 na rana, a lokacin da rundunar atisayen Puff Adder 11, suka samu bayanan sirri da ke nuni da cewa wadansu ‘yan bindiga a kan Babura an gansu sun nufi kauyen Pangu-Gari dake karamar hukumar Rafi.
Kwamishinan ya ce; a lokacin aka shirya tawaga guda zuwa wurin, inda aka yi musayar wuta a tsakanin ‘yan sanda da kuma ‘yan bindigar a daidai kauyen Tashan-Barau dake titin Tegina zuwa Minna.
Kwamishinan ya ce a lokacin musayar wutan ne aka kashe wani dan bindiga guda daya, wanda daga bisani aka gano sunansa wato Mohammed Garba, wanda yake mazaunin Unguwan Sani ne dake yankin Sabon Mariga a karamar hukumar Rafi. Sannan ba ya ga kashe shi, an samu bindigar AK-47 guda daya da alburusai dinta, da wani babur da ba a yi masa rijista ba kirar Bajaj.
Kwamishinan ya ce tuni aka kai gawar dan bindigar zuwa mutuware aka ajiye. Ya kuma tabbatarwa da al’umma cewa ‘yan sandan za su ci gaba da bankado bata gari da ‘yan bindigar, inda ya nemi hadin kan al’umma wajen ba su bayanan day a kamata domin saukaka musu ayyukansu.