Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce kin yarda da ya yi da sulhu da ‘yan ta’adda a jiharsa ya sanya ‘yan ta’addan ke zafafa kai hare-hare a jihar ta Kaduna, inda ya ce hakan ba zai sanya ya runsuna yana sulhu da ‘yan ta’adda ba, wanda ya ce a maimaikon hakan, zai tabbata da ana kashe ‘yan ta’addan ne da kawo karshensu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayani a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, inda Gwamna Nasir El-Rufai ya aminta cewa ayukan ‘yan bindiga da suka hada da kai hare-hare, kisan jama’a da satar mutane sun kara uzzura a jihar ne, sakamakon matsayar da ya yi na cewa ba zai yi sulhu da ‘yan ta’adda ba.
To sai dai gwamnan ya kara jaddada cewa “ba zai yiwu mu dauku kudin jama’a mu baiwa ‘yan ta’adda ba, kuma duk dan ta’addar da ya shiga Kaduna da mugun nufi na ta’addanci, to karshensa mutuwa ne.”
El-Rufai ya ce ya yi amanna cewa babbar mafita akan matsalar tsaro shi ne karfafa ayukan soji ta sama da kasa, ta yadda za su damar kawar da dukan ‘yan ta da kayar baya.