Dan wasan baya na Real Madrid Raphael Varane va zai samu damar fafatawa a kararwar zagayen farko da kungiyar sa za ta da Liverpool a gasar zakarun Turai na kusa da na kusa da na karshe ba, sakamakon harbuwa da Cutar Korona.
Ƙungiyar ce ta yi wannan sanarwa a shafukan ta na yanar gizo a yau talata.
Wannan ka iya zamowa babban kalubale ga Madrid ganin cewa tuni da ma kyaftin din tawagar Sergio Ramos sunan shi ya fita daga jerin yan wasan da za su fafata.
A yau talata ne Madrid za ta ziyarci Liverpool a filin wasa na Anfield don fafatawar zagayen farko na zakarun Turai wato Champions League.