Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya ce kakar bana “ita ce ta fi dacewa ya sauya kulob”.
Ana alakanta Pogba da komawa Real Madrid ko kuma tsohon kulob dinsa na Juventus.
Amma sai a watan Yulin 2021 kwantiragin dan wasan tsakiyar mai shekara 26 za ta kare.
“Ina tunanin komawa wani wurin domin tunkarar sabon kalubale,” a cewar Pogba.
“Shekara ta uku a Manchester kuma na taka rawar gani sosai, kuma na samu ‘yan matsaloli kamar yadda kowa yake fuskanta a ko’ina.
“Bayan kammala wannan kakar da irin abubuwan da suka faru, ina ganin ita ce kaka mafi kyau a gareni… ina ganin lokaci ya yi da zan matsa gaba domin fuskantar wani kalubalen.”
Sai dai duk da bayanan na Pogba, wanda shi ne ya fi kowa tsada a kulob din, Manchester United sun yi imanin cewa dan wasan zai kasance a Old Trafford a badi.
A watan Afrilu, kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya ce yana sa ran Pogba zai kasance a kulob din a kaka mai zuwa.