A daren yau Lahadi ne dai Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Spaniya ta lashe kofin zakarun turai na Champions League bayan markade Chelsea 4:0 a wasan karshe.
Tun a mintuna na 36 ne dai Barcelona ta jefa duka kwallayen da ta zura a wasan karshen da ta fafata.
Yanzu haka Barcelona ita ce kungiya ɗaya tilo a tarihin kwallon kafar duniya da ta lashe kofin zakarun turai na Maza da mata, wanda babu wata kungiya da ta taba haka.
Chelsea dai ta so nuna bajintar Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Ingila daya tilo ne wajen ganin ta yi wuff da kofin, tun bayan Arsenal da ta yi haka a shekarar 2007.
Yanzu haka dai a iya cewa Barcelonar ta mata ta share hawaye wa takwararta ta maza kenan bayan da suka gaza kai benten su a kowace gasa ta turai.