Ko shakka babu Sanata Dino, Melaye zai tsaya takarar zaben kujerar Gwamnan Jihar Kogi, wanda zai gudana a watan Nuwamba, idan baku manta ba Dino ya lashe kujerar Sanata a manyan zabukan kasar nan da suka gabata a wata Fabareru.
Ana saka ran Dino zai tsaya takara a karkashin inuwar babbar Jam’iyyar adawa ta PDP idan lokaci ya bayar.
To wai kuwa mai ya jawo raayin Sanata Dino Melaye, da son tsayawa takarar Gwamnatin Jihar Kogin, bayan ya samu ya kwaci kujerar Sanata a lokaci mai tsadar gaske?
Shin Jam’iyyar adawa ta PDP na da sauran damar karbar wata Jihar kamar Kogi a hannun Jam’iyyar mulki ta APC?
Zuwa yau baa ga Maciji a tsakanin Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da Sanata Dino Melaye, wanda hakan na daga cikin Hujjojin daya saka Sanatan ficewa daga Jam’iyyar APC kafin zabukan 2019, kuma hakan bai hana shi nasara ba.
To lallai fa idan Dino zai tsaya takarar Gwamna to dole zai ajiye kujerar sa ta Sanata, kafin ya shigo cikin wadanda zasu fafata a zabukan fidda gwani kafin babban zabe.
Lallai ko dai kujerar sa ta Sanata ko kujerar Gwamnan Jihar Kogi, ko kuma biyu babu.