Fitacciyar jaruma Fatima Isah Muhammad, wacce aka fi sani da Teemah Makamashi. Ta bayyana cewar, ita fa a yanzu babu wani abun da zai Hana ta fitowa a cikin fim, don haka babu wata rana da za ta daina yin fim, tun da sana’a ce a wajen ta.
Jarumar wacce a yanzu ta rikide ta zama yar kasuwa da ta ke shiga kasashe, domin gudanar da kasuwancin ta, wanda hakan ne ma ya sa ba a ganin ta a fim, ko kuma ake gani ta wuce yin fim din a yanzu.
Amma da wakilin mu ya ke yi mata tambaya a game da hakan sai ta ce.
“Babu wani abu da zai Hana ni yin fim, don har yanzu ma ina cikin harkar, don haka masu cewar harkar kasuwancin da na ke yi zai hana ni yin fim Kamar suna kashe mini kasuwa ne, domin duk abin da na zama a duniya, to ta dalilin fim na zama, don haka fim sana’a ta ce, wacce duniya ta sanni da ita, kuma har gobe ina cikin ta. Sai dai abin da na ke so mutane su sani ita harkar fim, za ka tsufa ko a dai na yayin ka, ko ka yi aure, amma shi kasuwanci za ka iya yi har ya’yan ka su gada” inji ta
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattijai zatayi tsari Mai kyau Kan kasafin 2022
Kazalika a cewar ta, “Don haka, yanzu ka ga na bude kanti ina sayar da kayayyaki kuma ina fita ina sayowa, kuma duk ta dalilin fim ne, don haka, harkar fim ta yi mini rana ta yi mini wando da riga, har da bargo ma ta yi mini, saboda haka babu abin da zan ce sai dai godiyar Allah.