Dan wasan Tsakiya na Kasa Naijeriya Peter Etebo, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Watford daga Stoke city.
Kungiyoyin biyu sun fitar da wannan sanarwar ce, a shafukan su na yanar gizo, a yau juma’a.
Kungiyar Watford ta fara wallafa cewa, ” Muna Murnar sanar da ku cewa, munyi nasaran daukan Peter Etebo, daga kungiyar Stoke City a kan yarjejeniyar zaman aro na tsawon kaka guda, da kuma zabin siyan shi. Barka da zuwa Kungiyar Watford Peter” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Dan wasan mai buga Lamba hudu a tsakiyar Fili, na da shekara 25 ne da haihuwa, Kuma ya fa-fa-ta wa kasa Naijeriya wasannin 38, Na manyan Yan wasan ta, ya yin da ya buga wasannin 19 na matasan Yan kasa dake da kasa da shekara U23.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dubun wani Mai shekara 90 ta cika
Tun bayan zuwasan kungiyar Stoke city a watan Yunin shekarar 2018, Etebo ya kwashe tsawon lokaci ya na zaman aro a kungiyoyin Getafe da Galatasaray, inda ya fa-fa-ta wa kungiyoyin a gasar Europa League.
Etebo dai ya fara taka Leda ne, a tsohuwar kungiyar sa da ke gida Naijeriya ta Warri Wolves, kafin ya sauya sheka zuwa Kungiyar Feirense ta kasar Portugal a shekarar 2016.
Lokacin da ya ke kungiyar Feirense ya tallafa wa kungiyar haurowa zuwa gasar Primeira Liga.