Wani mutun mai kimanin shekara 90 Mai suna Yusuf Yarkadir ya shiga hannun hukumar yaki da Sha da fataucin miyagun kwayoyin ta kasa NDLEA, bisa zargin saida wa matasan kauyen shi na Yarkadir dake karamar hukumar Rimi na jihar Katsina kwayoyin maye.
Lokacin da ake tambayan wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa, yana saida wa matasan kauyen, tabar wi-wi na tsahon shekaru 8.
A cewar Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi, ya ce, ” Ko da yake, wanda ake zargi ya ki bayyana inda ya ke samun kwayoyin, amma ya ce, ya yi kokarin barin sana’ar tashi tun da dadewa, sai dai bai yi nasara ba” inji shi
Awani cigaban Kuma, Jami’an hukumar ta NDLEA reshen jihar Ondo, sun yi nasaran kama wasu Matasa biyu, tare da wani dillalin miyagun kwayoyi, bisa zargin ta’ammali da haramtattun magunguna a babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalibai da Makaman Kwalejin Nuhu Bamalli da akayi garkuwa da su sun shaki iskar yanci
Matasan sun hada da Onyema Sunday mai shekara 16, da Yar uwarsa Onyema Amaka mai shekara 15, da aka kama su a hanyar Car dake birnin Akure, dauke da kwayar Tiramadol, da takai dauyin kilo 1.89 kgs, a ranar Litinin 5 ga watan Yulin wannan shekaran nan.
Ya yin da hukumar ta aka kama Kazeem Oluyede mai shekara 23, a yankin Eri Oba dake bababn birnin jihar, dauke da tabar wi-wi mai dauyin kilogiram 300grams, da kwayar Methamphetamine mai dauyin kilogiram 3.
Kazalika a dai wannan rana ce kuma, jami’an hukumar ta NDLEA su ka kama wata Mata Mai suna Maryam Musa, mai shekara 35 a yankin Igbara-Oke dake karamar hukumar Ifedole dake jihar, dauke da tabar wi-wi, mai dauyin Kilo 5.5kgs.
Bugu da kari a jihar Bauchi ma, rundunar ta NDLEA ta yi nasarar kama akalla Mutum 7 da ta ke zargi, dauke da miyagun kwayoyin daban-daban da su ka hada da: Diazepam, Exol-5, Rophynol, Tramadol, Codeine, da kuma tabar Wi-wi.
Wadanda hukumar ta baje kolin su a shelkwatar ta dake Bauchi sun hada da: Sunday Obi, Abba Abdullahi, Samuel John, Chioke Agu, Sani Musa, Alhaji Alhaji Baffa, da kuma Abubukar Saidu.
Comments 1