Shugaban Kasar Nijar Bazoum Muhammed sun kulla Yarjejeniya tare da gwamna Babagana Zulum na Borno kan yiwuwar dawo da Yan gudun hijira 130,000 gida Najeriya.
Bazoum Muhammed yace ” Mun gama shiryawa tsaf nan da watan Nuwamba zuwa Disamba na wannan shekarar Yan gudun hijiran Najeriya dake zaune a Diffa zasu koma Najeriya, kimanin Mutane dubu dari da talatin ne ke zaman gudun hijira a yankin.”
KARANTA:- Peter Etebo ya koma Kungiyar Watford dake Kasar England
Kasar Nijar dai, ta dauki sama da mutane dubu goma wadanda suka tsere daga Arewacin Najeriya a sanadiyyar rikicin Bokoharam.
A Jahar Borno, nan ne rikicin yayi kamari inda aka kashe mutane sama da dubu arba’in, sannan sama da miliyan biyu suka bace bat.
Hukumomin Jahar dai, suna iya bakin kokarin su don ganin wadanda suka bace sun koma gidajen su.
A cikin garin Diffa dake Kasar Nijar nan ne dai matattarar Yan gudun hijira, inda yawansu yakai kimanin mutane dubu dari uku kamar yadda Majalisar Dinkin duniya ta bayyana.