Wakilinmu Mu’azzam Yakubu Sanka
Hukumar karbar koken jama’a da Yaki da Al’mundahana ta jihar Kano, zasu binciki biyan albashin ma’aikatan gwamnatin jihar inji Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Ya bayyana hakan ne a wani taron da Hukumar ta gudanar kan dokokin ta da irin tsarin da take bi wajen aiki yana mai cewa suna zargin rashin gaskiya cikin biyan albashin ma’aikatan jihar Kano.
Rimin Gado, yace Hukumar ta lura da cewa akwai matsalolin karuwan albashin wasu ma’aikatan gwamnatin jihar a ‘yan kwanakin nan.
Yace wata matashiya dake aiki da Hukumar a kwanan nan ta samu kararrawar shigan albashin ta (alert) na kimanin Naira dubu 400 wanda yafi albashin ta sosai.
Haka kuma wani ma’aikacin Hukumar dake aiki a karamar Hukumar Gezawa shima ya samu irin kararrawar wacce ta nuna kudin da aka tura masa ya wucwe nashi albashin.
Tuni ma har sun mayar da kudaden zuwa aljihun gwamnati.
Banda wannan, Hukumar har wa yau ta samu labarin ire-iren karuwar kudaden biyan albashin ma’aikatan jihar Kano a wasu Hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar.
Don haka ne Hukumar ta kudiri aniyar yin binciken domin dakatar da lamarin.
Waya sani? kila hakan na da wata manufa, amma yayin da muka yi binciken zamu iya gano gaskiya da kuma wanda yake da hannu cikin lamarin.
Hakki ne da ya rataya a wuyan mu, mu tabbatar da anyi aiki bisa ka’ida tare da ganin cewa ayyukan gwamnati suna tafiya bisa gaskiya da adalci a dukkan matakai, inji Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Gado, yace idan har ba a yaki rashin gaskiya a dukkan sassan aiki ba, to fa Nijeriya zata cigaba da fama da matsala mai kama da wannan kuma ba zata taba cigaba ba.
Ya koka da cewa idan ba a dakatar da wannan yanayin ba, al’umar da zata taso nan gaba ba zata samu haske ba.
Yace rashin gaskiya yana barazana ga cigaban Najeriya don haka ne akwai bukatar ‘ya ‘yan ta baki daya su tashi tsaye wajen yaki da rashin gaskiyar.