Rahotannin dake shigowa yanzu yanzu na nuna cewa, Tsohon Ministan wutar Lantarki na Kasa Saleh Mamman, ya yanke jiki ya fadi a Babban birnin Tarayya Abuja.
An yi gaggawar kai shi wata asibiti ne tun a jiya Laraba, bayan samun sakon sanarwar Shugaban kasa Buhari da ya fitar kan sallamar Ministan daga aiki, tare da takwarar shi na fannin gona wato Sabo Nanono.
A cewar wata kafar yada labarai ta yanar gizo People’s Gazzate ta ce, Ministan ya yanke jiki ya fadi ne, bayan an bayyana Mai cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shi daga aikin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta kama Mutane 8 da zargin Kashe wani Mutum a Jigawa
Idan za’a iya tuna wa dai, Mamma ya kasan ce Ministan Wutan lantarki tun daga shekarar 2019, har izuwa jiya Laraba, da Shugaba Buhari ya yi kwas-kwarima a majalissar zartarwar shi .
Sai dai harkawo wannan lokaci na hada wannan rahoton, jaridar Blueprint ta ruwaito cewa, batasami ji ta bakin guda daga cikin masu taimakama Tsohon Ministan ba, domin tabbatar da lamarin.
A kwai Karin bayani….
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnan Jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tura sunan Shugaba da Mambobin Hukumar Kula da Harkokin Majalisa ga Majalisar Dokoki ta Jahar domin tantance wa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yan Jarida na Gwamnan Abba Anwar ya fitar a ranar 1 ga watan satumbar Shekarar 2021.
A cikin takardar da Gwamnan ya aikewa Zauren Majalisar, Gwamna Ganduje yace “domin tabbatar da bin dokar da Sashe na 4 karamin sashe na 1 na Majalisar Dokoki, Doka ta Shekarar 2011 Wanda yayi dai-dai da (1432), ta bada damar nada Shugaba da Mambobin Hukumar Kula da Harkokin Majalisa, Ina amfani da wannan damar domin turo sunayen don tantance wa domin nada su.”
Sunayen daya tura sun hada da; Nasiru Mu’azu Kiru a matsayin Shugaba daga Karamar Hukumar Kiru, da Ishaq Tanko Gambaga daga Karamar Hukumar Dala a matsayin Mamba, da Ali Abdu Doguwa a matsayin Mamba daga Karamar Hukumar Doguwa.
Sauran Mambobin Hukumar sun hada da; Salisu Abubakar daga Karamar Hukumar Makoda, da Isyaku Umar Mahmud Rurum daga Karamar Hukumar Rano, da Ladan Sabo Ahmad daga Karamar Hukumar Sumaila, da Gambo Ibrahim Mai Wada daga Karamar Hukumar Makoda.
Sai Ukashatu Bello Dambatta daga Karamar Hukumar Dambatta, da Nasiru Zakari daga Karamar Hukumar Kumbutso, gami da Sule Musa Musa Adnan daga Karamar Hukumar Warawa.
Daga karshe ya bukaci Majalisar data karbi sunayen cikin girmamawa gami da fatan Alkhairi.