Gwamnatin jihar Kaduna a yau Alhamis ta bada sanarwar dakatar da saffarar dabbobin zuwa wasu jihohin dake fadin kasar nan.
Mr Samuel Aruwan Kwamishinan cikin gida da kula da sha’anin tsaro na jihar ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanar wa da ya fitar a yau Alhamis.
Inda sanarwar ta ce ” Bayan tuntuban Kwararru, da kuma yin dubi akan sha’anin tsaro, Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta jigilan dabbobi zuwa cikin jihar daga wasu jihohi dake kasar nan”
KARANTA WANNAN LABARIN: Ministan da Shugaba Buhari ya kora ya yanke jiki ya fadi a Abuja
Ya kara da cewa, dakatarwar ya shafi shigo da dabbobi daga wasu jihohin zuwa jihar Kaduna, inda ya kara da cewa, dukkanin umarnin za su fara aiki ne nan take.
A cewar shi, Gwamnatin Kaduna ta na tunatar da al’uma cewa, jigilar Jakuna zuwa jihar babban laifi ne, kuma duk Wwanda aka kama, zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi.
Kazalika ya ce, Kasuwar Kawo dake ci mako-mako a kowace ranar Talata, a karamar hukumar Kaduna ta Arewa dake jihar, an dakatar da ita, nan take.
“Mu na sanar da al’uma cewa, dukakanin umarnin haramcin da muka bada, mun Sanya hukumomin tsaro domin su tabbatar da anbi dokar kamar yadda ya dace” inji sanarwar.
A wani labarin na daban.
Akalla Yan ta’adda guda 6 da ake kyautata zaton Yan Kungiyar Boko Haram/ISWAP ne, Rundunar Sojin Nigeria ta hallaka.
Daraktan yada Labaru na Soji Onyema Nwachukwu ya bayyana haka a cikin wata Sanarwa daya fitar a ranar Alhamis.
Ya kara dacewa, Rundunar Sojin ta kwato Bindiga kirar AK-47 guda 4 da Magazine na Harsashi da sauran su aka samu a wurin su.
Sanarwar mai taken ” Rundunar Soji ta Operation Hadin Kai ta Kashe Yan ISWAP guda 6.
Takardar tace ” Yan ta’addan Wanda suke akan hanyar Damboa-Bulabulin-Maiduguri sun yi arangama da Sojojin a Kukawa, inda suka kashe su.