By Ishaq Dabai
Yan bindiga sun saki dalibai biyar daga cikin ‘yan makarantar sakandiren gwamnatin Jeka Ka Dawo Ta Kaya, dake karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
A kalla dalibai 73 ne akayi garkuwa dasu a ranar laraba a cewar rundunar ‘yan sandan jihar.
Da yake magana a gidan talabijin na channels ta wayar tarho, tsohon kansila na mazabar Kaya, Yahaya Kaya yace ‘yar yayansa na daga cikin wadanda yan bindigar suka saka.
A cewar sa daliban guda biyar, sun dawo gida garin Kaya da misalin karfe daya na safiya ranar Alhamis.
Har yanzu yan bindigar basu bukaci kudin fansaba kafin su saki sauran daliban da suke rike dasu ba.
Satar daliban Kaya itace sata mafi girma da a kayi a yanki arewa.
A ranar laraba ne dai gwamnatin jihar Zamfara ta bada umarnin rufe dukkanin makarantun firamare dana sakandire dake fadin jihar duba da yanayin tsaron jihar ya kara ƙazanta.