By Ishaq Dabai
Hukumar Kula da tashoshin jirgin kasa ta Najeriya (NRC) ta samu koya baya ta bangaren fasinjoji, wadanda suka yi amfani da jirgin kasa daga Legas zuwa Kano, sakamakon mamakin ruwan sama da aka samu a Legas.
Manajan hukumar mai kula da yankin jihar Legas Mr Jerry Oche ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa cewa hukumar ta fara aikin jigilar kaya da mutane a karshe mako daga Legas zuwa kano kuma jirgin zai rika aikinsa a duk ranakun juma’a ne kawai.
Sannan ya bukaci yan Najeriya da su duba muhimmancin saukin sufurin da jirgin kasa yake da shi ta fuskar zirga-zirga da kuma sada mutum da duk inda yake son zuwa a fadin Nigeria.
Tikitin kudin jirgi dai daga mabanbantan tashoshi yana kamawa daga Legas zuwa Abeokuta tsadar sa naira 450 saukin sa kuma naira 350, daga Ibadan Zuwa Legas tsadar sa naira 850 saukin sa kuma naira 550 Edo tsakanin 1,200 zuwa 800, Oshogbo 1,1250 zuwa 850, Offa tsakanin 1,450 da kuma 950, Ilorin 1650 da kuma 1,100.
Kazalika farashin daga Makwa tsakanin 2,200 da kuma 1,450. Kutiwengi 2,500 da kuma 1,650; Akerri nair 2,650 zuwa
N1,750; Minna N2,800 da kuma N1,850; sai Serikinpawa N3,050 da kuma N1,950; Kaduna Junction N3,700 da kuma 2,400; Zaria N4,000 da kuma N2, 600 baya da haka tasha ta karshe itace jihar kano
Ina ake biyan naira 4,600 da kuma naira 2,959. Kamar yadda Oche ya zayyana.
Ya kara da cewa jirgin yana dauke da jama’an tsaro soja ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya, sannan yace jirgin yana kwashe sa’o’i 30 daga Legas zuwa kano.