Real Madrid ta tsara kwantiragi har bakwai iri daban-daban domin gabatar wa Kylian Mbappe a kokarin da ta yi na sayensa, kafin ranar karshe ta kasuwar ‘yan wasa, amma kuma kungiyar tana ganin dan wasan na Faransa mai shekara 22 zai zabi ya koma wurinta ne a 2022 bayan wa’adinsa ya kare da Paris St-Germain. (Sport – in Spanish)
PSG ba ta gabatar da tayi a hukumance kan sayen Cristiano Ronaldo duk da cewa ta tattauna a kan dan wasan mai shekara 36, kafin ya bar Juventus ta koma Manchester United. (Le10Sport)
Dan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, ya shawo kan Rennes ta bar shi ya tafi Real Madrid a bazaran nan duk da irin garabasar da PSG ta gabatar masa da shi da tsohuwar kungiyarsa. (AS)
Juventus tana son gina ‘yan wasanta yadda za su iya taka leda tare da dan gaban Argentina Paulo Dybala, mai shekara 27, bayan ta yarda Ronaldo ya koma United. (Calciomercato)
Dan wasan tsakiya Jesse Lingard, mai shekara 28, ya ki yarda ya zama dan West Ham na dindindin bayan da ya yi zaman aro a kakar da ta wuce, domin ya yi kokari ya samu gurbi a Manchester United. (90Min)
Comments 1