By Ishaq Dabai
Maitaimakin Daraktan Hukumar bunkasa fasahar nazarin Halittu ta kasa, NABDA, Mr Christopher Orji ya kashe kansa har Lahira a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa an dai samu Gawar Mr Orji’s cikin mawuyacin hali a rataye a jikin fankar dake dakinsa, inda yake zaune a gidan ma’aikata na gwamnatin tarayya a Lugbe Abuja, da misalin karfe 4 na yamma a ranar 30 ga watan Agusta.
Majiya daga ɓangaren da abun ya faru, tace hukumar ta NABDA ta bayyanawa manema labarai cewa tuni jami’an yan sanda suka dauki duk abinda ya kamata, da nufin binciko Musabbabin rasuwar Mutumin mai shekaru 59 a duniya.
Rahotonni sun nunar da cewa hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC ce ta gayyaceshi i zuwa ofishin su dake Abuja kafin ranar kuma sai Gawar sa aka ci karo da ita.
Baya da haka, daya daga cikin ma’aikatan hukumar, ya bukaci masu damuwa irin ta Orji da su daina kashe kansu.
Bayan an tuntubi mai rikon muƙamin shugaban bangaren sadarwa na NABDA, Nkiru Amakeze baice komai ba akan lamarin. Yana cewa ba zai iya magana ba.