Wataƙila Manchester United ta iya kawo ɗan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice baɗi, domin da alama Chelsea ta fasa nemansa. (Mirror)
Chelsea za ta ci gaba da sa ido kan mai tsaron bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde don duba yiyuwar sayen shi a watan Janairun 2022. (Evening Standard)
Ɗan wasan gaban Ingila Jesse Lingard ya yi watsi da tayin sabon kwantiragi domin ci gaba da zama a Manchester United.
A baya Lingard, wanda ya yi zaman aro a West Ham bara, ya buƙaci United ta bar shi ya canza ƙungiya domin samun damar buga wasa akai-akai. Kuma da ma kwantiraginsa da kulob din za ta ƙare ne ƙarshen kaka. Metro
Matashin ɗan wasan Ingila Jude Bellingham ya ce akwai yiwuwar zai tafi Liverpool daga Borussia Dortmund. (Star)
Har wayau Mirror ta ruwaito cewa Bayern Munich da Barcelona da Liverpool ta rige-rigen sayen ɗan wasan Red Bull Salzburg da ke Jamus Karim Adeyemi.
Tun ba a je ko’ina ba ɗan wasan yaci ƙwallaye shida a wasanni shida a kakar bana. (Bild, via Mirror)
Arsenal ta yi watsi da tayin Galatasaray ta Turkiyya kan Mohamed Elneny. (Sky Sports)
Ɗan wasan tsakiyar Real Madrid Marco Asensio ya ce baya buƙatar zuwa Tottenham ko AC Milan duk da ba ya samun yadda yake so a Madrid ɗin. (Marca)
Akwai yiwuwar Arsenal ta sallama wa Stuttgart da ke Jamus mai tsaron bayanta Konstantinos Mavropanos. (Bild, via Star)