Rundunar ‘yan sanda a Osun a yau Litinin ta gurfanar da wani mutum mai suna Yusuf Akintilo mai shekara 33 a gaban kotun Majistare dake Ile-Ife bisa zarginsa da satar kofar karfe guda biyar da kudinsa ya kai naira dubu casa’in (90, 000).
Dan sanda mai gabatar da kara, Sunday Osanyintuyi, ya shaidawa kotu cewa; wanda suke kara ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Oktoban 2020 a titin Olonade dake Ile-Ife a Osun.
Osanyintuyi ya ce kofofin na wani mutum ne mai suna Olafare Augustine.
Ya bayyana cewa laifin na shi ya sabawa sashe na 383 da 390 na dokar miyagun laifuka ta Osun ta shekarar 2002.
Wanda ake zargi ya musanta aikata laifin.
Wanda ya ke bai wa wanda ake zargi kariya, Ben Adirieje, ya nemi da a bai wa wanda yake karewa beli. Inda ya bada tabbacin cewa wanda yake karewa ba zai tsallake beli ya gudu ba, zai kawo wadanda za su tsaya masa tsayayyu.
Alkaliyar kotun Majistare din, A.I. Oyebadejo daga karshe ta bada belinsa akan naira 50,000 da mutum daya da zai tsaya masa da yake da kudin.
Oyebadejo ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya yi rantsuwa kuma ya zama yana da muhalli a inda kotun take.
Ta kuma ce wanda zai tsaya masa dole ya zama yana da aiki kuma zai kawo fasfo dinsa na yanzu guda uku.
An dage shari’ar har zuwa 27 ga watan Satumba.