Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kai hari Makarantar Sakandare ta Kasa, dake garin Nkume na karamar Hukumar Njaba a Jihar Imo, bayan ayyana dokar zaman gida-gida da yan masu fafutukar kasa kasar Biafra IPOB suka yi.
Rahotanni na nuna cewa, yan bindigan sun mamaye harabar makarantar lokacin da wasu dalibai ke shiga jarabawar kammala karatun sakandare na yankin nahiyar Afrika ta Yamma wato WASCE, na shekarar 2021, sannan suka dakatar da rubuta jarabawan.
Sai dai harkawo hada wannan rahoton ba a Sami Cikakken bayani kan afkuwar lamarin ba, amma an samu labarin cewa, yan ta’addan sun lalata wasu kadarori yayin harin a makarantar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan zuwan Shugaba Buhari, Al’umar Imo sunyi Fatali da Umarnin zaman gida na Kungiyar IPOB
Ko da majiyar jaridar dimokuradiyya ta tuntunbi Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam, bai dauki wayar shi ba, kuma ya kasa amsa sakonnin da aka tura masa.
Idan za’a iya tunawa, Kungiyar IPOB ta ba da umurnin cewa, yankin ya kasance yana kula da dokar zaman gida a kowace ranar Litinin, don nuna goyon bayan ga shugabanta, Mazi Nnamdi Kanu, wanda ke tsare a hannun jami’an hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.
Comments 1