By Ishaq Dabai
Rahotonni sun bayyana cewa a kashe wasu lauyoyi a jihar Imo da Darlington Chidume Odume, wanda aka fi sani da Omekagu.
Daya daga cikin Wanda abin ya rutsa da shi, wanda aka ce matar sa ‘yar sanda ce da ke aiki,matar tace ta samu labarin an kira shi zuwa Bar kimanin shekaru biyar da suka gabata.
Kisan nasa ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan da aka kashe wani limamin cocin Anglican, Rabaran Emeka Merenu a gidan sa dake unguwar Iheteukwa, karamar hukumar Orsu, wanda har yanzu ba a san ko su wanene ba.
An bayyana cewa maharan sun harbi Odume ne a gaban wani babban kanti a Umudara Amaifeke Orlu, dake karamar hukumar Orlu ta jihar.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa Marigayin Odume mashahurin lauya ne a Orlu wanda ke kula da wasu kararrakin wadanda aka kama dangane da tashin hankalin da ya dabaibaye yankin.
A cewar majiyar, wanda abin ya rutsa da shi, tuni aka garzaya da shi zuwa asibiti a yankin amma aka ki karbarsa inda kuma aka tura shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Imo, sai dai kuma Orlu, ya rasu a kan hanyar zuwa asibitin koyarwa, An jefa dukkan al’umma cikin makoki, “in ji majiyar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, CSP Michael Abattam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Kwamishinan‘ yan sandan, Hussaini Rabiu ya ba da umarnin yin cikakken bincike a kan lamarin dan cafke wadanda suke da hannun akan lamarin,” in jishi.