Tawagar shugabannin kungiyar kasashen yammacin Africa ECOWAS/ CEDEAO ta gana da jagororin da suka kwace mulki a kasar Guinea domin gabatar ma su da sakon kungiyar na neman soja su gaggauta mka mulki cikin wata shida.
Tawagar da ta kunshi Shugaba Nana Akufo-Ado na Ghana da Shugaban Cote d’Ivore Alassane Ouattara sun gana da shugabannin sojan Guinea ne a wani Otel dake birnin Conakry.
Da isar su Otel din ne kuma jagoran sojan na Guinea da suka kwace iko a Guinean Laftanal Kanal Mamady Doumbouya ya isa Otel din cikin wata motar soja mai sulke, tare da rakiyar sojoji da suka rufe fuskokinsu.
Ganarwar dai sun yi ta ne bayan da Kungiyar ta ECOWAS ta ja kunnen sojan da suka kifar da Gwamnatin farar hula ta Alfa Conde a ranar 5 ga wannan wata da muke ciki, da su hanzarta mika mulki.
Kazalika kungiyar ta sanya musu haramcin tafiya, ga kuma toshe asusun kudadensu da kaddarorin kasar.
Juyin Mulki sojan na Guinea ya jefa shakku cikin dorewar Dimokuradiyya a wasu kasashen Afrika da har yanzu ake samun juyin mulkii da rana tsaka.