Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga takwaran shi na Algeria Abdelmadjid Tebboune, kan rasuwar tsohon shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika.
Shugaban, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar jiya Asabar, ya kuma jajantawa iyalan tsohon shugaban, da kuma Al’umar kasar baki daya, yayin da suke juyayin rashin “fitaccen shugaba,” wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 20 a baya.
Shugaba Buhari ya ce Bouteflika babban jarumi ne, da ya taka rawar gani a yakin basasar da ta kai ga samun ‘yancin kan Algeria. Inda ya kara da cewa, Tsohon Shugaban kasar yaba da gudummawa sosai ga ci gaban ƙasar Algeria.
Kazalika ya ce, A bangaren Afirka kuwa, Bouteflika ya kasance Mai kishin Nahiyar Afrika, kuma ba za a manta da abin da abun da ya bari ba, na tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya, tsakanin Algeria da kasashe irin su; Eritrea da kuma Habasha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum 2 Sun Mutu, 21 sun jikkata ya yin da aka farmaki Motar Taliban
A karshe Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan Tsohon Shugaban kasar na Algeria, inda kuma ya mika ta’aziyar sa, ga jama’ar Algeria a lokacin da suke cikin bakin cikin rashin Tsohon Shugaban su Abdelaziz Bouteflika.
A wani labarin Kuma na daban.
Tsohon mai magana da yawun Shugaban Kasa Doyin Okupe ya gargadi Shuwagabancin Jami’iyyar PDP akan sake tsaida Dan takarar Shugaban Kasa daga yankin Arewa a zabe Mai zuwa na Shekarar 2023, Yana mai cewa hakan zai iya sanyawa ta sake rasa kujerar ta.
Ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da yan Jarida a ranar Asabar a Abuja.
Okupe ya bayyana cewa, Shirin da Jami’iyyar PDP ta yi na tsaida Dan takara daga Kudu a zaben Shugaban Kasa na Shekarar 2019, shine ya kawo cikas a nasarar Jami’iyyar.
Ya kara dacewa, har yanzu wasu mutane daga Jami’iyyar na yunkurin kawo Dan takara daga yankin Arewa a zaben Shekarar 2023.
Ya ce manyan yan siyasa na fita daga Jami’iyyar, a dalilin Shirin gabatar da Dantakara daga yankin Arewa.
Ya bayyana tsoron cewa, Jami’iyyar zata iya sake faduwa kafin Shekarar 2023, idan har canja Sheka ya cigaba da wakana.
Okupe ya kara dacewa, “matsalar canja sheka da ake samu a Jami’iyyar PDP baya da alaka ko kadan da rikice-rikicen dake faruwa a Jami’iyyar. Wannan dama yana faruwa ne a duk lokacin da aka tunkari Babban zabe a cikin Kasa.
“Duk Wanda suka fita daga Jami’iyyar suna da wata matsala da Shuwagabancin Jami’iyyar, musamman ta fuskar bangarantar da takara.
“Matsalar bangarantar da takara a Jami’iyyar bai kamata ace, ya zama abunda zai sanya a rika futa, domin an nada Kwamiti dazai lura da wannan matsalar, kuma nan bada jimawa ba zai kammala aikin sa, gami da gabatar da bincike da yayi.
“Bangarantar da takarar da Jami’iyyar PDP ta fara tun Shekarar 1998, ya faru ne a dalilin hasashen da Jami’iyyar tayi na kasancewa a saman mulki, amma daga lokacin data rasa ikon mulki a Shekarar 2015, komai sai ya canja gaba daya, Kuma dole a yi dubi akan wannan cigaba da aka samu.