By Ishaq Dabai
‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da malamin makarantar Larabci da addinin Musulunci a yankin Kuregu dake karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10 na dare lokacin da ‘yan fashin suka kutsa kai cikin al’umma garin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ko a ranar 19 gawatan Janairu, 2021 sai da aka sace Farfesa Aliyu Mohammed na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi, da ke zaune kusa da al’umma garin na kuregu sai da aka biya adadin da ba a bayyana ba a matsayin kudin fansa kafin ya sake samun ’yanci.
Wani mazaunin garin Kuregu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa mutanen biyu da aka kashe ‘yan garin ne.
Ya kara da cewa wadanda abin ya shafa suna wurin da bai dace ba saboda ‘yan fashin sun zo ne suna neman gidajen masu hannu da shuni a cikin al’umma lokacin da suka ci karo da wadanda abin ya rutsa dasu sannan suka harbe su kafin su sace malamin makarantar addinin Musulunci a cikin al’ummar garin.
Koda aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Jalige yayi alkawarin zai kira waya bayan ya samu baya nai daga yankin amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton.