Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Umma Shehu, ta bayyana cewar, ita fa ba za ta fito a cikin fina-finan kudu ba, saboda ya saba wa addinin ta.
Jarumar ta ce “Ni Musulma ce, kuma addini na bai yarda da wasu abubuwa da a ke yi a cikin fina-finan kudu ba, kamar rungume-rungume da wasu abubuwa da suka saba wa addini na” inji ta
“Ni mace ce gaba zan duba, idan na duba abin ba zai taba ni ba sai na yi, ba wani abu ba ne. Amma fa abu ne na addini, yanzu komai mutane idan an tashi sai su ce addini” a cewar ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za muyi Amfani da 5G don Dakile Matsalar Tsaro, inji Gwamnatin Tarayya
Kazalika Umma Shehu ta ce, “Wallahi duk abin da namiji ya yi ado ne, ba kamar mace ba. Mace duk abin da ta yi yana nan a ajiye, wata rana za a fada wa ya’yan ki, don haka dole ne mu mata mu rinka kiyaye yadda za mu tafiyar da rayuwar mu, don gudun bar wa ya’yan mu abin fada. “
Assalamualaikum