Babban sufeton rundunar yan sandan na kasa Usman Baba ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba rundunar za ta dauki Sabin jami’ai guda 20,000.
Baba ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Ibadan, yayin wata ziyarar aiki da ya Kai wa gwamnan Oyo Seyi Makinde a jihar.
IGP ya ce, rundunar yan sanda ta kuduri aniyar kara karfin ta, don kara inganta tsaron cikin gida a Nigeria.
Baba ya Kuma bayyana cewa, matsalolin da ke kawo tsaiko dangane da aikin daukar sabbin jami’an, an warware shi, inda ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da izinin yin rajista.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun da yasa bazan fito a Fina-finan Kudu ba, inji Umma Shehu
Kazalika ya ba da tabbacin kowace jiha da karamar hukuma, za su amfana kamar yadda jami’an za su yi aiki a karamar hukumar su bayan samun horo daga rundunar.
Baba ya bayyana cewa ziyarar tasa ita ce yin mu’amala da masu ruwa da tsaki kan aikin jami’an yan sanda na cikin al’umma da sauran batutuwa masu mahimmanci.
Ana shi bangaren Gwamna Makinde na jihar Oyo, ya yi alkawarin ci gaba da hadin gwiwa da jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin dakile Matsalar Tsaro a jihar.