Ƙungiyar Dattawan Arewan Nigeria a ranar Talata, ta yabawa Gwamnonin yankin Arewa, da suka ƙi amincewa da tsarin karba-karba na shugaban ƙasa ya zuwa yankin kudu, kamar yadda Kungiyar Gwamnonin Kudu ke nuna buƙatar hakan.
Mai Magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewar Baba-Ahmed ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi ga taron manema labaru Kaduna a ranar Talata, inda ya bayyana buƙatar Gwamnonin Kudu na amsar shuwagabancin ƙasar a shekarar 2023 a matsayin abinda ba za’a taɓa yarda ba.
Baba-Ahmed yace Gwamnonin Kudu suke haifar da tsaiko a Dimokuraɗiyyar ƙasar ta hanyar neman kujerar shugaban ƙasa, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda za ta dauki jami’ai 20,000, inji Usman Baba
A cewar sa, duk wani shugaba da za’a zaɓa, dole ayi hakan ta hanyar dimokuraɗiyya, ba ta hanyar barazana da nuna fin ƙarfi.
Yace “munyi wannan maganar a makonni biyu da suka gabata, muna farin ciki ganin yadda Gwamnonin kudu sun yi magana akan hakan. Tsarin karɓa-karɓa baya cikin kundin tsarin mulkin ƙasar, amma wannan bai sanya ya zama ba halattacce ba, ko kuma a matakin siyasa kaɗai za’a iya hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin da ya sa ba zan fito a fina-finan Kudu ba, inji Umma Shehu
“muna janyo hankali akan cewa, akwai yiwuwar Gwamnoni 17 na kudu su haɗa kawunan su, domin cin mutuncin ƴan arewa, ta hanyar sanya dokar hana kiwo a fili, tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa da sauran al’amurra.
“Gwamnonin kudu suke kawo tsaiko a tsarin dimokuraɗiyya. Abinda dimokuraɗiyya ta yarda dashi shine akwai jami’iyyun siyasa, akwai ƴan takara, akwai kuma masu kaɗa kuri’a, duk wanda yaci zabe, sai ya zama ɗan takara, wanda daganan sai ayi sasanci.”
Baba-Ahmed yace Dattawan Arewa nason ƴan Nigeria dasu fahimci cewa har yanzu ana mutunta dimokuraɗiyya, a saboda haka bazasu, bazasu iya nuna yadda shugabancin ƙasa zai kasance.