By Ishaq Dabai
Hukumar kula da gidan waya ta Najeriya (NIPOST) tace ta kara kudin da take aikawa da sakonni daga Naira 50 zuwa Naira 250 don samar da ingantaccen aikin hukumar a kasar.
Mista Friday Aba, Manajan Shiyyar NIPOST ta jihar Enugu, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron abokan ciniki a jihar don tunawa da “Ranar Post ta Duniya” da ake yi kowace shekara a ranar 9 ga watan Oktoba.
Aba yace NIPOST ta shirya taron a fadin tarayyar don sanar da abokan ciniki kan karin farashin jadawalin farashin NIPOST na cikin gida.sanan ya bayyana cewa bita ta karshe da aka yi shekaru 16 da suka gabata, Saboda da haka yana cewa yin bita ya zama dole don baiwa NIPOST damar samar da ingantaccen aikin hukumar ga abokan cinikin ta.
“Hakanan muna son yin amfani da damar don sanar daku sake dubawa na ƙimar kuɗin aikewa da sako na NIPOST daga
N50 zuwa N250.“Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta amince da bita don aiwatarwa.
Ya lura cewa baya ga hanyar bayar da aikin hukumar na gargajiya, NIPOST ta canza zuwa sabon ingantaccen aiki wanda ya haɗa da ayyukan kuɗi, kasuwanci da dabaru.
A nasa jawabin, Shugaban taron, Mista Chris Ejiogo, yace yin bitar ta zama dole saboda farashin wasu kayayyakin ya hauhawa saboda annobar cutar COVID-19.
Comments 1