By Ishaq Dabai
wasu da ake zargin sun sha giya mai dauke da guba a yankin Orenburg na kasar Rasha tayi sanadiyar mutuwar mutane 17 daga cikin 33, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Juma’a.
Wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka da dama a cikin Urals, kilomita 1,200 kudu maso gabashin Moscow.
Gwamnan yankin Denis Pasler ya yi kira ga mazauna yankin dasu guji siyan barasa. A cewar Pasler, an gudanar da bincike mai yawa na shagunan dake siyar da barasa don cire marasa kyau daga yaduwa. “Har sai an kammala sakamakon bincike, shan barasa na iya zama barazana ga rayuwa,” in ji gwamnan.
A cewar hukumomin, an kwace kwalabe sama da 1,000, duk da cewa barasa da ake magana a bayyane bata bambanta da sauran barasar ba.
Masu binciken sun riga sun cafke mutane uku da ake zargi, daga cikinsu akwai wani mutum mai shekaru 29 wanda aka ce shiya shirya samarwa ba bisa ƙa’ida ba a cikin birnin Orsk, inda ‘yan sanda suka yi imanin sun gano ginin da aka yi muggan abubuwan sha.
“A wasu lokuta, an gano yawan abin dake cikin abin ya ninka sau uku zuwa biyar fiye da adadin da ake kashewa.”Mahukunta sun bukaci mutane dasu gaggauta ganin likita bayan sun sha barasa, domin a wasu lokutan ana daukar kamar awa daya tsakanin jin rashin lafiya da mutuwa, in ji su.