Akwai dimbin jami’an tsaro a rumfunan zabe daban -daban a babban birnin jihar Filato, da kewaye, yayin da ake shirin gudanar da zabe a dukkan kananan hukumomi 17 a ranar Asabar.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nigeria (NAN), wanda ya ziyarci wasu yankuna, ya ba da rahoton cewa, Jami’an sojoji, ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya (NSCDC) da sauran hukumomin tsaro an jibge su a rumfunan zabe daban -daban don jefa kuri’a.
Wasu daga cikin yankunan da aka ziyarta sun hada da Tudun Wada, Rayfield, Mai Adikwo, Abattoir, Goradong, Gura Topp, Rukuba Road, Agwan Rukuba, da sauran su, duk a karamar hukumar Jos ta kudu da Jos ta Arewa na jihar.
ASP Ubah Ogaba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, ya shaida wa NAN cewa, an tura aikin ne da nufin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NIPOST ta Kara Kudin shiga da kashi 400
Kazalika rundunar Yan sanda ta gargadi masu laifi da za su iya tayar da fitina a lokacin zabe da su daina, domin duk wanda aka samu zai fuskanci fushin doka.
A nasa bangaren, DSC Chris Longbit, Jami’in Hulda da Jama’a na Filato hukumar NSCDC, yayi kira ga masu kada kuri’a da su kasance masu zaman lafiya a lokacin zabe.
Ya kara da cewa, rundunar ta kuma tura dakarunta zuwa dukkan sassan jihar, don dakile karya doka da oda.