Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta ƙasa ta bayyana cewar, ta soke sunayen mutane dubu sittin 62,698 da suka buƙaci a sake yi masu rajista.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a jawabin da yayi, a lokacin wani taron gaggawa na jami’iyyun siyasa a Abuja a ranar Juma’a.
Yace an gano hakan ne a lokacin da hukumar ke kan aiki tuƙuru domin gano bayanai da za’a yi amfani dasu a zaɓen Anambra.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsaurara Matakan Tsaro a jihar Filato
Yace, “A jahar Anambra, kimanin mutane dubu ɗari 138,802 suka kammala rajistar su, ciki harda waɗanda suke so a canja masu rumfunan zaɓe, da kuma waɗanda suke son a musanya masu katikan zaɓe, musamman wanda suka rasa nasu ko ya lalace kamar yadda doka ta tanada.
A lokacin da muke ƙoƙarin kammala rajistar muka gano wasu sun sake yin rajistar ne, wanda a hakane muka gano cewar mutane dubu 62,698 wanda tuni sunyi rajista, amma sun sake yin wata kuma doka ta hana yin haka.
Yakubu ya ƙara dacewa, hukumar bazata futo da katikan zabe na waɗanda suka sake rajista, inda ya jaddada cewa, har yanzu nasu yana aiki.
Ya kuma sanar dacewa hukumar ta shirya tura a ƙalla ma’aikata dubu 26,000, inda ya nuna rashin jindaɗin sa na ƙarancin ma’aikatan gabanin basu horo a sati mai zuwa.
Comments 1