By Ishaq Dabai
Kwamandan rundunar, hukumar kula da hadura ta kasa FRSC, na jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, yace hanyar Bauchi zuwa Darazo ita ce mafi hatsari a jihar zuwa yanzu a shekarar 2021 wanda ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da dama.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan gangamin na wayar da kai na watanni 2021 mai taken: “A kiyaye saurin gudu, a guji tafiye -tafiyen dare kuma a ji daɗin ƙwarewar hanya,” an sanya tutar a babban filin ajiye motoci na tsakiyar Bauchi.
“Babban abin daya dame mu shine babbar hanyar Bauchi zuwa Darazo wadda muka gano a matsayin mafi hadari a jihar. Wannan saboda direbobin dake bi ta wannan hanyar ba koyaushe suke yin taka-tsantsan ba, kuma galibin hadurran da ake samu na faruwa ne sakamakon yawan gudun wuce sa’a da tafiye-tafiye cikin dare.
“Hanya ta biyu mafi hatsari ita ce hanyar Bauchi zuwa Gombe. Muna kira ga masu ababen hawa dasu kasance masu taka tsantsan don kawo mafi karancin hadurran dake haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, ”in ji shi.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Abdulkadir Ibrahim ya wakilta, a cikin jawabinsa yayin kaddamar da gangamin ya yabawa hukumar ta FRSC a jihar kan yadda ta kasance mai kokari matuka wajen mayar da martani ga haddura ta hanyar bada agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
Gwamnan wanda ya kuma yabawa hukumar FRSC kan kula da zirga -zirgar ababen hawa a wurare masu mahimmanci a cikin jihar musamman a lokutan bukukuwa, sannan gwamnatinsa tayi alkawarin tallafawa hukumar FRSC don cimma nasarar aikin ta na rage hadurran hanyoyi wanda galibi ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi a jihar. .